Farillan Sallan da adadin su

 Farillan Sallah sune ayyuka mafiya girma da muhimmanci a cikin Sallah.

Yana da matukar muhimmanci ga dukkan musulmi yasan farillan Sallah, domin kiyaye su da kyau. Barin daya daga cikin su yana lalata Sallah gaba dayan ta. Ba abin da yake gyara Sallah bayan barin farilla.

Gasu kamar haka;


  1. Niyya; A zuciya, bai sai mutum ya furta ba, kudirce yin Sallar a zuciya kadai ya wadatar.
  2. Kabbarar harama; fadin "Allahu Akbar" a yayin da ka fara Sallah, wannan shine mabudin Sallah.
  3. Tsayuwa domin ta; wannan Kabbarar a tsaye ake yinta, sai dai in da lalura da mutum ba zai iya tsayuwa ba.
  4. Karatun Fatiha; karanta suratul Fatiha a kowacce raka'a dole ne.
  5. Tsayuwa domin sa; karatun Fatiha a tsaye ake yi, sai dai in da lalurar mutum ba zai iya tashi ba.
  6. Ruku'u; sunkuyawa da kugu, da dafe gwiwoyi da hunnu, farilla ne.
  7. Dagowa daga Ruku'u, dagowa daga wannan sunkuyawar shima farilla ne.
  8. Sujjada; sunkuyawa da sanya goshi da hanci, tafin hannaye, da gwiwoyin kafa a kasa farilla ne. Ana yinta sau biyu a kowwace raka'a.
  9. Dagowa daga sujjada; dagowa daga wannan sunkuyen farilla ne.
  10. Nutsuwa; a lokacin da kake gaban ubanjigin ka Allah, kawar da kome da tsayar da hankalin ka ga bautarwa Allah.
  11. Sallama; fadin Assalamu Alaikum warahmatullah, a karshen Sallah farilla ne.
  12. Zama domin ta. Wannan sallama a zaune ake yinta sai dai in da wata lalura da zata hana zaman.
  13. Jeranta farillai; jeranta farillai daga niyya sai karatun Fatiha sai ruku'u sai.... Zuwa karshe farillhaka.
  14. Daidaituwa; baya halatta me Sallah ya dinga jujjuyawa kai, ko hannu, ko kafa, ko ma tafiya, ko wani motsi da ba ya cikin aikin allah.
Ya kamata mu daure mu rike farillan Sallah, dan gudun yin kuskere a Sallah, hakan yasa Sallar mu ta dinga baci.

Muna maraba da shawarwarin Ku, da kuma gyararrakin Ku, domin anfanar musulmi baki daya🙏

Comments