Mustahabban Sallah

 Mustahabban Sallah

Suna daraja na uku acikin ayyukan Sallah, duk da cewa barin mustahabban sallah baya bata Sallah, amma sallar wanda ya cika mustahabban sallah da wanda bai cika ba, ba zai taba zuwa daya ba, in ana maganar daraja da lada.

Sabi da haka yana da matukar muhimmanci musan mustahabban sallah domin muyi cikkakiyar Sallah irin wadda Allah yake so.

  1. Daga hannaye yayin harama; su zama sun yi kafada da kunnuwansa, kuma yatsun hannuwan sun mike sama.
  2. Rabbana wa lakal hamdu; gamamu da mai Sallah shi kadai.
  3. Fadin Amin; bayan karatun Fatiha ga mai Sallah shi kadai da mamu liman shi kuma a karatun boye zai ce amin.
  4. Tasbihi a cikin ruku'u; "Subhana rabbiyal aziim" ( sau uku ) ko "Subhaakal laahumma rabbana wa bihamdika, allahummag firlii".
  5. Addu'a a cikin sujjada; ana son yin addu'a acikin Sujjada.
  6. Tsawaita karatun; ana son tsawaita karatu a Sallar asuba, sai sallah azzahar.
  7. Gajerce karatu; ana son a gajerce karatu a cikin Sallar la'asar da magriba.
  8. Takaita karatu; ana son takaita karatu a Sallar Isha'i
  9. Tsawaita karatun surar raka'ar farko akan ta biyu; ana son karatun Sallah raka'ar farko tafi ta biyu tsayi.
  10. Al-kunutu a boye; kafin rukuk,'u a raka'a ta biyu cikin Sallar asuba
  11. Banbanta tsayin tahiya ta farko da ta biyu; ana son ta biyu tafi tsayi akan ta farko
  12. Motsa dan yatsa; acikin tahiya mutum ya dinga motsa dan yatsansa, manuniya.
  13. Yin sallamar a bangaren dama; kallon bangaren dama yayin sallama.


Wannan sune mustahabban sallah, yin su kuma shi yake cika Sallah, Sallah mafi kololuwar daraja a gurin Allah.


Allah ya bamu ikon kiyayewa, da yin Sallar da Allah yafi so.

Muna maraba da shawarwarin Ku, da kuma gyararrakin Ku, domin anfanar musulmi baki daya🙏




Comments