Salatul Khusufi (sallar gushewar/canzawar hasken Rana ko wata

 Shinfida

Kmar kullum addini musulunci baya taba barin mu akowacce yanayi sai ya nuna mana yadda zamuyi, da kuma bamu mafita a kowanne yanayi, shi yasa aka tanadar mana salatul khusufi (Sallar gushewar hasken rana ko wata).

A duk lokacin da muka tashi da wani bakon yanayi na gusher hasken rana ko wata, ko canzawar yanayin su abin da zamuyi shine Sallar khusufi.

Mene Salatul Khusufi?

ALKUSUFU: Shine gushewar dukkan hasken Wata ko Rana, ko wani sashin hasken, ko kuma jirkicewar hasken su.

Sallar Khusufi sunnace mai karfi, a gurin imam malik ba'a sallar khusful kamar (khusufi na wata) a cikin jam'i, kowa zai yi tasa ne, kuma ba'a ruku'i irin na khusufil nahar (khusufin rana) ana yinta kamar sauran nafifuli.

Lokacin da ake yinta

Lokacinta shine da zarar anga wannan kusufin har zuwa lokacin da zai yaye.

Ba'a yin ta a lokacin da ranar data yi khusufi tafadi, ko watan dayayi khusufi ya gushe.

Yadda ake yinta

Babu kiran sallah ko ikama

Raka'a ta farko

  • Kabbara; Za'ayi kabbara
  • Karatun Fatiha; wannan karatun a sirrance za'ayi.
  • Karatun sura; kamar baqra, shima a sirrance.
  • Ruku'u; mai tsayi kamar na karatun da akayi.
  • Dagowa daga ruku'u; tare da fadin sami'allahu liman hamida.
  • Fatiha; za'a sake yin Fatiha a sirince
  • Karatun sura; za'a kara wacce batakai ta farko ba, amma mai tsayi kamar al'imran, a sirrace ita ma.
  • Ruku'u; mai tsayi kamar dadewar karatun da akayi.
  • Dagowa daga ruku'u; da fadin sami'al lahu liman hamda.
  • Sujjada; a wannan karan za'ayi sujjada biyu, kamar yadda ake a kowacce sallah.

Raka'a Ta Biyu

  • Karatun Fatiha; wannan karatun a sirrance za'ayi.
  • Karatun sura; kamar nisa'i, shima a sirrance.
  • Ruku'u; mai tsayi kamar na karatun da akayi.
  • Dagowa daga ruku'u; tare da fadin sami'allahu liman hamida.
  • Fatiha; za'a sake yin Fatiha a sirince
  • Karatun sura; za'a kara wacce batakai ta farko ba, amma mai tsayi kamar ma'ida, a sirrace ita ma.
  • Ruku'u; mai tsayi kamar dadewar karatun da akayi.
  • Dagowa daga ruku'u; da fadin sami'al lahu liman hamda.
  • Sujjada; a wannan karan za'ayi sujjada biyu, kamar yadda ake a kowacce sallah.
  • Tahiya da Sallama; za'ayi tahiya da sallama.

Ba'a khudba amma babu laifi ga yin hakan.

Ana son a wannan lokacin a yawaita istigfari da anbaton Allah da kyawawan ayyuka.  

Muna maraba da shawarwarin Ku, da kuma gyararrakin Ku, domin anfanar musulmi baki daya🙏

Comments