Salatus safri (sallar matafiyi) da hukunce-hukuncen ya

 Shimfida

Kamar ko da yaushe musulunci yana shimfida mana hanyar da zamuji dadin Rayuwa a duniya da lahira, da kuma saukaka mana hanya.

Allah bai sanya mana tsanani a Addini ba.

Mecece Sallatul musafiri (sallar matafiyi)

Sallah ce domin sauki ga matafiya.


Yaushe Ake Sallar Matafiyi

A lokacin da mutum zai yi tafiya akalla kamar kilomita 83.

Mutum zai fara sallar bayan ya fita daga garin su, bawai zai fara tun a gida ba.

Kuma zai ajiye a sanda ya dawo ko ya kusa karasawa gida.

Yadda ake sallar matafiyi

Asuba; Raka'a biyu

Azzahar; Raka'a biyu

La'asar; Raka'a biyu

Magriba; Raka'a uku

Isha'i; Raka'a biyu.


Abin lura

•Ba'a kasru a sallar magriba, Sallar Asuba kuma tana nan yadda take.

•Matafiyi zai iya sallah akan abin hawansa idan yana tsoron wani abu, idan zai iya kallon Alqibla sai ya kalla, idan ba zai iyaba ya kalli ko ina.

Haka idan zai iya sujjada ko ruku'u in kuwa ba zai iya ba sai yayi ishara.

•Matafiyi zai iya hade azzahar da la'asar, lokaci daya magriba da isha'i a lokaci daya.

•Idan matafiyi yayi niyyar kwana hudu a wani gari ko sama da haka, ko bai san lokacin da zai kai ba da zai bar garin, zai dinga kasru har zuwa lokacin da zai bar gari.

•Idan matafiyi yayi sallah a bayan (liman) mazaunin gida to dole ya cika sallar sa.


Muna maraba da shawarwarin Ku, da kuma gyararrakin Ku, domin anfanar musulmi baki daya🙏

Comments