Sallar Idi da hukunce-Hukuncen ta

 Shinfida

Wannan sallah tana daga cikin manyan abubuwan da addinin musulunci ya tanada, domin karfafa soyayya da sada zumunci tsakanin musulmi.

An shar'anta musulmi da su zo daga mabanbantan gurare, domin haduwa da juna, da kuma bautarwa Allah Daya da suka yada dashi, suke kan tafarki daya domin sa.

A wannan Rana ana son kowa yayi wanka, yasa kaya masu kyau domin haduwa da yan uwansa musulmi.


Sannan su tafi a kafa, suna masu anbaton sunan Allah ubanjigin su "Allahu Akbar, Allahu Akbar, laa ilaaha illallah"

"Allahu Akbar, Allahu Akbar, walillahil Hamd"

Zasu yi ta maimaitawa har su isa massallaci.


HUKUNCIN SALLAR IDI

Sallar idi sunna ce, bata  bukatar ramuwa idan ka rasa ta, sai dai bubu laifi idan ka yi ta bayan ta wuce ka.

Ba'a kiran sallah ko ikama, sannan a fili ake karatun ta.


Lokacin Sallar Idi

Ana yin ta ne a lokacin da rana ta billo zuwa lokacin da tayi ziwali.


Yadda ake Sallar idi 

Raka'a biyu akeyi a sallar idi

Niyya; zaka kudire Niyyar yin sallar idi a zuciyarka.

RAKA'AR FARKO

  1. Kabbarar harama; za'ayi kabbara tare da harama.
  2. Kabbara shida; za'ayi kabbara shida bayan kabbarar harama, ba tare da daga hunnu ba.
  3. Karatun Fatiha; a bayyane za'ayi karatun
  4. Karatun sura; shima a bayyane anfi son karanta suratul A'ala.
  5. Ruku'u; bayan kammala karatun sura.
  6. Dagowa daga ruku'u; tare da fadin "Sami'allahu liman hamida".
  7. Sujjada; sujjada guda biyu kamar ko wacce sallah.


RAKA'A TA BIYU

  1. Kabbarar mikewa; za'ayi kabbara tare da mikewa.
  2. Kabbara biyar; za'ayi kabbara biyar bayan kabbarar mikewa, ba tare da daga hunnu ba.
  3. Karatun Fatiha; a bayyane.
  4. Karatun sura; a bayyane anfi son karanta suratul shamsu.
  5. Ruku'u; bayan kammala karatun sura.
  6. Dagowa daga ruku'u; tare da fadin "Sami'allahu liman hamida".
  7. Sujjada; sujjada guda biyu kamar ko wacce sallah.
  8. Zaman tahiya Da sallama; a wannan raka'a za'a kammala sallah da yin tahiya da sallama.
  9. Khuduba; bayan kammala sallah liman zai khudba, zai ja hankali da nasiha ga al'ummar musulmi.


Idan babbar sallah ce, liman zai zo da abin yankan sa, ya yanka ko kuma ya soke, ta inda mutane zasu shaida.


  • Ana son mutum ya sanja hanya daban da wacce yazo yayin komawa, ba ta inda yazo massallaci ba (daga liman har mamu).
  • Ana son mutum yayi wanka, yasa kaya musu kyau, ya tafi massallaci yana mai ambaton Allah. 
  • "Allahu Akbar, Allahu Akbar, laa ilaaha illallah"
  • "Allahu Akbar, Allahu Akbar, walillahil Hamd"
  • Idan karamar sallah ce ana son mutum yaci dabino ko wani abu kafin zuwa massallaci.
  • Idan babbace ya kame bakin sa har sai an dawo.


Comments