Sallar jana'iza (Sallar Gawa) da hukunce-hukuncen ta

 Sallar jana'iza (Sallar Gawa)

Itace sallar da akewa mamaci bayan ya mutu. 


Yadda ake Sallar jana'za (Sallar Gawa)

Idan Namiji ne mamacin Sai liman ya tsaya saitin kan sa, Idan Mace ce Sai liman ya tsaya tsakiyar ta daidai.

Kabbara hudu ake yi da Addu'o'i bayan wanke mamaci.

Kabbara ta farko; tare da daga hannu, sannan suratul Fatiha da sura a sirrance.


Kabbara ta biyu; ba tare da daga hannu ba, da salati ga Annabi Muhammad ﷺ,


Kabbara ta uku; ba tare da daga hannu ba, da addu'a ga mamaci kamar haka;

"ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﺤﻴﻨﺎ ﻭﻣﻴﺘﻨﺎ ﻭﺷﺎﻫﺪﻧﺎ ﻭﻏﺎﺋﺒﻨﺎ ﻭﺻﻐﻴﺮﻧﺎ ﻭﻛﺒﻴﺮﻧﺎ ﻭﺫﻛﺮﻧﺎ ﻭﺃﻧﺜﺎﻧﺎ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻣﻦ ﺃﺣﻴﻴﺘﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺄﺣﻴﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻹﺳﻼﻡ، ﻭﻣﻦ ﺗﻮﻓﻴﺘﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺘﻮﻓﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻪ ﻭﺍﺭﺣﻤﻪ ﻭﻋﺎﻓﻪ ﻭﺍﻋﻒ ﻋﻨﻪ، ﻭﺃﻛﺮﻡ ﻧﺰﻟﻪ ﻭﻭﺳﻊ ﻣﺪﺧﻠﻪ، ﻭﺍﻏﺴﻠﻪ ﺑﺎﻟﻤﺎﺀ ﻭﺍﻟﺜﻠﺞ ﻭﺍﻟﺒﺮﺩ، ﻭﻧﻘﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﻳﺎ ﻛﻤﺎ ﻳﻨﻘﻰ ﺍﻟﺜﻮﺏ ﺍﻷﺑﻴﺾ ﻣﻦ ﺍﻟﺪﻧﺲ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﺑﺪﻟﻪ ﺩﺍﺭﺍً ﺧﻴﺮﺍً ﻣﻦ ﺩﺍﺭﻩ، ﻭﺃﻫﻼ ﺧﻴﺮﺍً ﻣﻦ ﺃﻫﻠﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﺩﺧﻠﻪ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻭﺃﻋﺬﻩ ﻣﻦ ﻋﺬﺍﺏ ﺍﻟﻘﺒﺮ ﻭﻣﻦ ﻋﺬﺍﺏﺍﻟﻨﺎﺭ، ﻭﺍﻓﺴﺢ ﻟﻪ ﻓﻲ ﻗﺒﺮﻩ ﻭﻧﻮﺭ ﻟﻪ ﻓﻴﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ

ﺗﺤﺮﻣﻨﺎ ﺃﺟﺮﻩ ﻭﻻ ﺗﻀﻠﻨﺎ ﺑﻌﺪه"

Kabbara ta hudu; ba tare da daga hannu ba, sannan addu'a ga mamaci, ko al'ummar musulmi, ba laifi idan ma baiyi addu'a a wannan karan ba.

Sannan sallama.

Muna maraba da shawarwarin Ku, da kuma gyararrakin Ku, domin anfanar musulmi baki daya🙏





Comments