SALLAR ROKON RUWA (SALATUL ISTISKA'A)

 Shinfida

Addinin musulunci har kullum yana kawo mana mafita daga dukkanin matsala, kamar haka Allah ya tanadar mana wannan sallah, don lokacin da muka shiga matsala ta karancin ruwa, wanda hakan yake haifar da fari da yunwa.


Sallar roƙon ruwa sallah ce da ake yinta lokaci zuwa lokaci ma'ana lokacin da aka shuka amfani kuma aka sami ƙarancin samun ruwa na wasu ƙwanaki da har Amfanin gona ya fara bushewa ko lalacewa.


RAKA'A TA FARKO

  • Kabbarar harama; za'ayi kabbara tare da harama.
  • Kabbara shida; za'ayi kabbara shida bayan kabbarar harama, ba tare da daga hunnu ba.
  • Karatun Fatiha; a bayyane za'ayi karatun
  • Karatun sura; shima a bayyane anfi son karanta suratul A'ala.
  • Ruku'u; bayan kammala karatun sura.
  • Dagowa daga ruku'u; tare da fadin "Sami'allahu liman hamida".
  • Sujjada; sujjada guda biyu kamar ko wacce sallah.



RAKA'A TA BIYU

  • Kabbarar mikewa; za'ayi kabbara tare da mikewa.
  • Kabbara biyar; za'ayi kabbara biyar bayan kabbarar mikewa, ba tare da daga hunnu ba.
  • Karatun Fatiha; a bayyane.
  • Karatun sura; a bayyane anfi son karanta suratul shamsu.
  • Ruku'u; bayan kammala karatun sura.
  • Dagowa daga ruku'u; tare da fadin "Sami'allahu liman hamida".
  • Sujjada; sujjada guda biyu kamar ko wacce sallah.
  • Zaman tahiya Da sallama; a wannan raka'a za'a kammala sallah da yin tahiya da sallama.
  • Khuduba; bayan kammala sallah liman zai khudba, zai ja hankali da nasiha ga al'ummar musulmi. Yana tunasar da mu tane su koma ga Allah, su bar aikata zunubai, domin suna daga sanadin yankewar rahamar ubangiji.
  • Sanan ya juya ya kalli Alkibla; yana mai juwa mayafin sa, bangaren dama ya koma hugu hagu ya koma dama. 
  • Sannan ya fara addu'a; yana mai daga hannun sa, mutane suma su daga hannayen su. Yana rokan  Ruwa, yana me cewa;
 اللهم أغثنا، اللهم أغثنا، اللهم أغثنا"  sau  uku. 


اللهم اسقنا غيثًا مغيثًا هنيئًا مريئًا غدقًا مجلًا سحًا طبقًا عامًا نافعًا غير ضار، تحيي به البلاد وتغيث به العباد وتجعله يا رب بلاغًا للحاضر والباد"
    Wannan tana daga addu'ar da manzon Allah yayi.
      "اللهم أنبت لنا الزرع، وأدر لنا الضرع، واسقنا من بركاتك" 
        "اللهم اسقنا الغيث ولا تجعلنا من القانطين"
          Zai dinga yin addu'a yana mai maimaita naci da kaskantarwa da kai ga Allah.
            Ba'a son sanya kaya masu ado, ana yinta da safe kafin rana tayi ziwali.

            Comments