Sallar tsoron Makiya da yadda ake yinta

 Sallar Tsoro (Salatul Khauf)

Kamar yadda muke yawan fada, kuma kowa ya sani, addinin musulunci ya shinfida mana tsarin Rayuwa mai kyau da tsari a rayuwar duniya, sannan mu samu babban rabo a lahira.

Shi yasa dukkan hukunce-hukuncen addinin musulunci ya dace da bukatar mu, don Allah bai sanya addinin sa ya zamo da kunci ga mutane ba.

Daga cikin bukatun mu aka saukaka mana nau'in wata sallah domin tsaro, a lokacin da ake tsoron Makiya ko makamancin haka.


Mece Sallar Tsoro (Salatul khauf)

Sallah ce da akeyi domin gadi da tsare wani abu da zai iya cutar da Al'ummar musulmi lokacin da suka sakankance da bautar ubanjigin su.


Anyita a zamanin annabi (saw) domin gadi da tsaro daga abokan yakin da suke jira musulmi su tada sallah, sai sallah su far musu da yaki.


Umarni da siffar yadda za'ayi sallar tsoro yazo a Al'qurani suratun nisa'i (101-104)


Yadda ake Sallar Tsoro

1-Anayin raka'a biyu-biyu ga kowacce sallah, amma banda magriba, ita raka'a uku ake.

2-Mutane zasu rabu shashi biyu

3-Liman zai yi sallah da sashi na farko Raka'a daya, sannan ya tsaya a tsaye.

4-Mamu zasu karasa raka'a daya alokacin da liman yake tsaye, sannan suyi sallama, su tashi su tafi.

5-Daya sashin zasu zo sai liman yayi raka'a daya dasu sannan yayi tahiya yayi sallama.

6- Mamu zasu tashi su cika raka'a daya suyi sallama.

Comments