Sharddan Sallah

 MENENE SHARADAN SALLAH

Shardan sallah sune abubuwan da idan suka cika sallah da hukunce-hukuncen suna cika, idan basu cika ba sallah bata cika.

Wannan sharadai sun kasu biyu;

Sharadin wajabcin ta; idan suka cika sallah tana wajaba (tana zama dole) idan basu cika ba sallah bata wajaba

Sune kamar haka ;

  1. Isar kiran annabi (saw) zuwa ga musulunci;  Idan kiran musulunci bai je wa mutum ba ko ina yake a fadin duniya, sallah bata wajaba akan sa. 
  2. Musulunci; musulunta tana wajaba idan kiran annabi saw yazo, kuma kasancewar ka musulmi sallah tana wajaba akan ka.
  3. Balaga; sallah bata wajaba akan yaro, amma ana so a horar dashi yin sallah da yin ta akan lokaci.
  4. Hankali; sallah bata wajaba akan wanda hankalin sa ya gushe, amma banda wanda ya sha giya ko abin bugarwa.

  1. Shigar lokaci; wayancen sharadan sun tabbata dole sai lokacin sallar ya shiga sannan sallah take wajaba.
Sharadin ingancin ta;
  1. Tsarkin jiki; wannan ya hada da tsarki, daga fitsari bayan gida, maziyyi ko wanka, don janaba haila da sauran su.
  2. Tsarkin tufa da guri; tabbatar da kawar da duk wata najasa da ta shafe su.
  3. Fuskantar Alqibla; dakin Allah ka'aba, amma awasu lokacin akwai sauki akan haka.
  4. Sitirta Al'aura; namiji daga cibiyar sa zuwa giwar kafa, mace kuma dukkan ta al'aurace banda fuskarta da tafin hannu da kafa.
  5. Aluwala; Sallah bats inganta sai da Aluwala. 
  6. Niyya; dole sai da niyyar yin sallah domin Allah sannan Sallar ka take inganta.
  7. Barin magana; mai sallah dole ya bar yin magana, sai karatu da zikirorin da ake acikin sallah.
  8. Barin kowanne aiki; baya hallata mutum ya dinga jujjuya jiki, acikin sallah.

          Muna maraba da shawarwarin Ku, da kuma gyararrakin Ku, domin anfanar musulmi baki daya🙏

          Comments