Sujjadar mantuwa (sujudis-sahwi)

 


Sujjadar mantuwa (sujudis sahwi);

 Ana kiranta haka domin ana yinta ne idan akayi kuskuren dadi ko ragi a sallah cikin mantuwa. Amma idan mutum yana sane ya dada ko rage wani abu acikin sallah sallarsa ta baci.

Ba'adi; ita ce sujjadar da ake yin ta bayan an yi kari a sallah, ana yi bayan an gama Sallah an yi sallama sai ayi sujjada guda biyu.


Kabli; itace sujjadar da ake yi bayan anyi ragi a cikin Sallah, ana yin ta kafin ayi sallama, raka'a biyu.


Abin lura

  1. Mantuwa: ana sujjadar bayan sallama ko kafin sallama ne idan akayi mantuwa ba da gangan ba, mutumin da ya rage ko dada wani Abu acikin Sallah yana sane ba mantuwa ba Sallar sa ta baci.
  2. Dadi; wanda yayi dadi acikin sallar sa zai yi sujjadar bayan Sallah (ba'adi), idan ya manta zai mayar ko bayan shekara ne. Wanda ya dada raka'a daya ko biyu zaiyi sujjada bayan Sallah (ba'adi) duk sanda ya tuna ko da bayan shekara ne, idan aka dada raka'a kamar ta adadin Sallar, Sallar sa ta baci.
  3. Kokonto; wanda yake kokonton cikar Sallar sa, to kamar tabbatar da rashin cikarta ne. idan raka'a dayace ko biyu zai cika, sannan yayi sujjada ba'adi. Idan sunnace daga biyu zuwa sama (ban da sunna daya kawai) zai sujjada biyu kafin sallama.
  4. Ragi; ana sujjadar kafin sallama (kabli) ne idan aka rage sunnoni biyu ko sama da haka, sai dai manta sunnar bayyana karatu ko boyewa.
  5. Ana sujjadar bayan sallama (ba'adi) a madadin sujjadar kafin sallama (kabli); idan sai bayan sallama aka tuna  anyi ragi, to sai ayi sujjadar ba'adi (sujjada bayan sallama) a madadin ta.
  6. Manta sujjadar kafin sallama (kabli) lokaci me tsaho; idan mutum ya manta sujjadar kabli har sai da ya fita daga massallaci ko bayan wani lokaci zai sanja Sallah gaba dayanta.
  7. Farilla; ba'a sujjada bayan sallama (ba'adi) ko kafin sallama (kabli) don barin farilla, za'a cika farillar kafin sallama, sannan ayi sujjadar bayan sallama (ba'adi). idan ya manata har yayi sallama, sai ya sanja sallah gaba daya.
  8. Mamaita surar Fatiha sau biyu; da mantuwa zai yi sujjada bayan sallama (ba'adi) idan yana sane Sallar sa ta baci 
  9. Dawowa da baya; idan mutum ya manta karatun sura har ya tafi ruku'u baya hallata ya dawo domin yin sa, Hakama ma manta zaman tahiya, idan mutum ya mike daga sujjada ba zai dawo ba, sai dai yayi sujjada kafin sallama (kabli) don barin zaman tahiyar da boye karatu, sai sujjada bayan sallama (ba'adi) don bayyanawa.

Kammalawa

Wannan suna cikin hukunce-hukuncen sujjadar mantuwa wanda ya kamata mu sani domin gyara Sallar mu.


Muna maraba da shawarwarin Ku, da kuma gyararrakin Ku, domin anfanar musulmi baki daya🙏

Comments