Sunnonin Sallah

Sunnonin Sallah sune ayyuka da suke mataki na biyu a ayyukan Sallah.

Yana da kyau musan sunnonin  Sallah domin kiyaye su da kyau, sunnonin Sallah sune kamar haka;


  1. Ikama; fadin "Allahu Akbar, Allahu Akbar, Ashhadu An La’ilaha ilal Lah, Ashhadu anna Muhammadan Rasulullah, Hayya alal Salah, Hayya alal falah, Qad Qamatus Salatu, Qad qamatus Salah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’ilaha ilal Lahu” kafin tayar da Sallah.
  2. Karatun sura; bayan karatun Fatiha
  3. Tsayuwa domin ta; a tsaye za'ayi karatun surar.
  4. Boye da bayyanawa; ana boye karatu a Salloli kamar Azzahar da La'asar, ana bayyana karatun a salloli kamar Magriba, Isha'i da Asuba.
  5. Kabbarori banda kabbarar harama;  dukkan kabarori sunnah ne banda kabbarar harama ita farilla ce. 
  6. Fadin "sami'allahu liman hamidah" bayan dogawa daka ruku'u.
  7. Tahiyoyi biyu; zama bayan sujjadoji guda biyu, bayan  raka'a'oi biyun farko da kuma zaman tahiyar sallama.
  8. Zama domin su; yin tahiya a zaune sunna ne.
  9. Gabatar da karatun Fatiha kafin karatun sura; fara karatun Fatiha kafin na sura sunna ce.
  10. Sallama ta biyu data uku; duk karin sallama bayan ta farko "Assalamu Alaikum warahmatullah" sunna ce
  11. Bayyana sallama; yin sallama a bayyane ba a boye ba sunna ce.
  12. Salati ga manzon Allah (saw); yin salati ga annabi a zaman tahiyar karshe, sunna ce.
  13. Sujjada akan dukkan gabobin takwas; hanci, goshi, tafin hannu biyu, yatsun kafafuwa, da gwiwar hannu.
  14. Sitira; Sanya sitira sunna ce ga Wanda yake sallah shi kadai ko liman ana bukatar ya sanya suturah a gabanshi, domin baiwa mai wucewa damar wucewa ta bayan suturar. Amma banda Wanda yake Sallah a bayan liman.

 

Ana bukatar duk wanda zai yi Sallah yazo da wayannan ayyuka, domin suna da matukar muhimman ci acikin Sallah.


Muna maraba da shawarwarin Ku, da kuma gyararrakin Ku, domin anfanar musulmi baki daya🙏

Comments