Taimama Da Hukunce-hukuncen ta

 Shifida

Addinin musulunci ya shinfada mana tsari wand zamuyi Rayuwa mai dadi da tsari a duniya, a lahira kuma mu samu kyakkyawar makoma.

Shi yasa a addinin musulunci babu abin da zai zame mana tsanani, kome an tsara mana shi dai-dai da bukatun mu.

Wannan shi yasa aka halatta mana taimama a madadin Alwala don kar mu shiga halinn kunci a lokacin da bamu da ruwa ko wata lalurar zata hana mu anfani da shi.

Mene Taimama

Taimama itace; Shafar fuska da hannaye a wuri mai tsarki ta yana yi kebantacce.

Allah yayi umarni da taimama  Suratul Ma'idah, aya ta:6

Yazo A hadisin manzon Allah (saw);

''An bani abubuwa biyar da ba'a ba wani ba kafin ni; An taimakamin da tsoro (ma'ana sanya tsoronsa a zukatan makiya) na tafira tsawan wata guda, kuma an sanya min kasa ta zama wurin sallah da kuma tsarki, duk inda wani mutum daga cikin al'ummata sallah ta riskeshi to ya yi sallar shi'' a wata riwayar ''To anan inda yake masallacinsa yake da kuma abin tsarkinsa''. Bukhari, Hadisi na: 335, Muslim Hadisi na: 521.

Abubuwan da suke halatta taimama

Ana taimama idan ba'a samu damar yin Alwala ko wanka, da dalilai kamar haka;

1-Rashin Ruwa: 

Lokacin da babu ruwa ko kadan da zakayi auwala dashi.

2-Rashin ishashshen Ruwa: 

Idan akwai ruwa amma ba ishashe ba, wanda akwai bukatar sha ko wata lalura.

3-Cutuwa; 

idan mutum yana jin tsoron cutuwa idan yataba ruwa, ko yana da cutar da take tashi idan ya taba ruwa.

4-Rashin Lafiya; 

Idan mutum yayi nisa da ruwa kuma bazai iya motsawa zuwa gare shi ba, kuma babu mai motsa shi, ko kawo ruwan gareshi.

Abunda ke Bata Taimama; 

duk abinda yake bata alwala yana batsa taimama. Sai dai Taimama sallar farilla daya ake yi da ita, sai dai ana iyi yin nafila da ita, ko biyan sallolin da ake bin ka.

Yadda Ake Taimama

•Zaka fara daura niyyar yin Taimama.

 •Sannan ka wara yatsun hannayanka biyu ne sai ka buga a kasa, sai ya dan karkade.

•Sanan sai ya shafi fuskassa da cikin tafikan hannunsa, zai game ko'ina na fuskarsa, har karkashin gemu.

•Sai kuma ya shafi hannayansa zuwa wuyan hannu (Ku'i), idan yana da zobe sai ya cire domin shafar ta game ko ina.

Ban-Bancin Aluwala da Taimama

1-Aluwala da ruwa ake yinta

Taimama kuma da kasa

2-Ana sallolin farilla da yawa da Auwala daya Idan bata karye ba

Taimama sallar farilla daya ake yi da ita, sai dai ana iyi yin nafila da ita, ko biyan sallolin da ake bin sa.

3-Aluwala ta hade wanke hannu faska, hannu, shafar kai da hanci, kuskurar baki, Wanke kafa da ruwa.

Taimama shafar hannu da shafar shafar fuska da kasa.

4-Auwala ita ce asalin abin da ake yi, taimama ana yin ta idan ba'a samu damar yin Alwala ko wankan tsarki ba.

Muna maraba da shawarwarin Ku, da kuma gyararrakin Ku, domin anfanar musulmi baki daya🙏




Comments