Tsarki da Hukunce Hukuncen Saa a Musulunci

Shimfida

Muna sane da cewa addinin musulunci yana koya mana abubuwa kyawawa ta Inda zamuji dadin rayuwar mu da wayanda suke tare damu a duniya da lahira.

Shi yasa tsafta tana daga cikin cikar imanin dukkan musulmi, tsarki babban abin da yake banbanta musulmi da Wanda ba musulmi ba a fagen tsafta.

 Menene Tsarki

Shine tsaftace jiki da tufa daga kazantar da take fita daga mafita guda biyu, gaba da baya.

Rabe-Raben Tsarki

Tsarki kala biyu ne 

  1. Tsarkin tufaShine tsarkake abinda ya taba jiki ko tufafi ko kuma wuri. ana wanke inda najasar ta taba ko a wanke duka idan ta fantsama.
  2. Tsarkin Kari; Shine tsarkin abinda ya fita daga dayan mafita guda biyu, kamar fitsari, maziyyi, maniyyi, gayadi, jinin al'ada da jinin haila. (Banda tusa)

Wannan ya rabu gida biyu;

Babba da karami

  • Babban kari; shine Hadasul Akbar; Shine kamar fitar maniyyi, ko saduwa, ko daukewar jinin al'ada ko na biki, Ana kiran shi babbane domin ba'a tsarkaka daga gareshi sai an yi wanka.
  • Karami Hadasul Asghar; wanda yake tsarki ko alwala ta wadatar, kamar fitsari ko maziyyi.


Abin da ake tsarki dashi shine 

  • Ruwa mai tsarki; Mai tsarki mai sarkake waninin sa, Wanda kamarsa bata canza ba ko dandanon sa ko launi, kamar maiko, ko sabulo ko wani Abu da ya sabawa al'adar ruwa. Amma kamar kasa ko tabo, gansakuka ko ganye da sauran su. basa gurbata shi. Yadda zakayi anfani da ruwa wajan wanke bayangida ko fitsara shine mutum ya wanke hannunsa na hagu kafin ya sa a wurin da zai wanke, sannan sai ya wanke wurin fitsari. Daga nan kuma sai ya fara wanke wurin bayan gida musamman idan ya katse, ana bukatar mutum ya wanke al'aurar sa baki dayanta musamman idan maziyyi ne ya fita.
  • Dutsena biyu kuma shine dutste. idan mutum bai sami ruwanba sai ya yi da duwatsu a kalla guda uku, idan ya ga na ukun ya fito a bushe ba wata laima shikenen, idan kuma akwai laima to sai ya kara su kai biyar wuturi ake bukata (3,5,7,9…) wannan kuma ana yinshi a fitsari ko bayan gida, sannan idan ka sami ruwa ba sai ka sake ba, wannan hukunci shi ake kira Istijmari, ka samu ka hada duka a lokaci guda.


Ladabin tsarki

  1. Addu'aAddinin musulunci ya tanadi addu'a a dukkanin ayyukan mu, domin samun tsoro daga abubuwan ki. addu'ar da addinin musulunci ya tanada yayin shiga ban daki shine; بِسْمِ اَللهِ، اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ اَلْخُبُثِ وَالْخَبَائِثِ Ma'ana: Da sunan Allah, Ya Allah lalle ni ina neman tsarinka (Ka tsareni) daga aljanu maza da kuma aljanu mata. 
  2. Fara Gabatar Da Kafar Hagu Lokacin Shiga; Ana son mutum ya fara gabatar da kafar haugu lokacin da zai shiga bayan gida 
  3. Fara gabatar da kafar dama lokacin fita; a lokacin fita kuma mutum zai fara gabatar da kafar dama.
  4. Tsugunawa; ba'a mutum ya yi fitsari ko bayan gida a tsaye, sai dai idan wurin kangone ko yana tsoron fitarin ya fallatso masa, sannan ba wanda zai ganshi ya samu ya yi a tsaye.
  5. Buya; Yana wajaba ga mai biyan bukata ya boye inda mutane baza su ganshi ba.
  6. Suturta jiki; Ana son kada mutum ya yaye al'aurar sa tun yana tsaye, sai ya tsugunna ya yi dab da kasa sai ya daga suturarsa, domin ba'a yarda wani ya ga al'aurar wani ba
  7. Bada karfi ga kafar hagu yayin biyan bukata; anfi so mutum ya fi bayar da karfinsa a kan kafarsa ta hagu.
  8. Bude cinyoyi; Ba'a son mutum yasa matattsiyar tufa wacce zata matse cinyoyin sa, don kada najaza ta bata kayansa, ko ya kasa kawar da ita yadda ya kamata.
  9. Nisantar gurin ruwa; musulunci bai yadda mutun ya yi fitsari ko bayan gida a inda ruwa yakeba ko kusa dashi, dan wannan zai haifar da cututtuka.
  10. Gujewa magana; ba'a magana yayin biyan bukata, said da wata lalura. tarar iska; 
  11. Ba'a son mutum ya tari iska lokacin da zai yi bayan gida a dawa (daji); hakan zai busowa jama'a warin bayan gidansa, kenan sai ya yi nesa, ya kuma duba ina iska take kadawa.
  12. Kaucewa Rami; Ba'a yarda idan za ka yi fitsari ko bayangida ka yi aramiba saidai idan kai ka haka, domin bakasan mekecikin ramin ba.
  13. Nesa Da Jama'a; ana bukatar dukkan wanda zai yi bayan gida ya yi nesa da jama'a ta yadda ba za su ganshiba kuma ba za su ji nishin shiba
  14. Kaucewa Alkibla; wato inda mutum yake kallo lokacin sallah, kuma kada ya juya mata baya, wannan idan a dajine, amma idan a gidane to da sauki.

Abubuwan da ba'a yi sai da tsarki

  1. SallahBaya halatta mutum yayi sallah ko wacce irice ba tsarki.
  2. Dawafi; Baya hatta mutum yayi dawafi sai da tsarki.
  3. Daukar Al'qurani; Baya halatta mutum ya dauki Al'qurani sai da tsarki.

     
    Muna maraba da dukkanin shawarwarin Ku da kuma gyararrakin Ku domin anfanar musulmi baki daya🙏



Comments