Azumi da kaffara ga mai ciki da mai shayarwa

Idan mata masu ciki  da masu shayarwa suna fuskantar barazana ga lafiyar su data abin da suke dauke da shi lokacin watan Ramadan. Yana hallata su kar suyi azumin watan Ramadan.

Malamai sun yi sabani akan Shin zasu rama azumin ne ko zasu ciyar. Sai suka tafi akan;

  • Shin za'a dauke su a cikin marasa lafiya da matafiya? Kamar yadda Allah yace "Kuma wanda ya kasance marar lafiya ko cikin tafiya sai yayi adadin wasu kwanakin (daidai yawan wadanda ya sha)" Bakara aya ta 185
  • Ko za'a daukesu a matsayin wayanda Azumi yake da wahala a kansu? Kamar wayanda Allah yace "Kuma akan wadanda suke yinsa da wahala, akwai Fansa; ciyar da miskini"  Bakra aya ta 184

To kenan anan akwai fahimta biyu da maslaha biyu.

  •  FAHIMTA TA DAYA; Masu ciki da shayarwa suna a matsayin marasa lafiya.
  • MASLAHA; Zamu tafi akan tafiyar mai ciki da mai shayarwa suna cikin marasa lafiya ne, don haka zasu rama azumin da suka sha mai makon ciyarwa. Wannan shine jumhur mafiya yawan malamai. kuma ra’ayin Imam Auza’i da Imam Hasanul Basari da Ibrahim an-Nakha’i da Ataa, da imamuz-zuhuri da kuma Imam Malik. Kuma wannan shine ra’ayin wadansu daga cikin magabata kamar su Ibn Taimiyya da almajiransa. Daga cikin malamai na kusa wadanda suka tafi akan wannan fahimta akwai ibn Baz da Al-uthaimin da sauransu.


  • FAHIMTA TA BIYU; Masu ciki da shayarwa suna a matsayin wayanda Azumi yake da wahala a Kansu.
  • MASLAHA; to sai mu tafi akan fahimtar Wayanda suk tafi akan mai ciki da mai shayarwa suna cikin wayanda azumi yake wahala akan su kamar tsofaffi. Dalilinsu kuwa shine fadin Allah ta’ala: “Kuma akan wadanda suke yinsa da wahala, akwai Fansa; ciyar da miskini" bakara aya ta 184. Suka ce wannan ayar ta hada da tsofaffi da ba za su iya yin azumi ba, da mai ciki da mai shayarwa. Don haka babu ramuwa akansu sai dai ciyar da miskini. wannan ita ce fatawar Abdullahi Dan-umar da Abdullahi Dan-abbas da Ishaq bin Rahawaih. Sannan shaykh Nasiruddeen Albani a cikin littafinsa Irwaa al-Ghaleel, da kuma almajiransa a cikin littafin Sifatus-Saum-an-Nabiyi, sun tafi akan cewa fatawar bin Umar da bin Abbas babu wanda ya saba musu a cikin sahabbai, don haka za’a iya cewa kamar ijima’i ne na jamhurin sahabbai baki daya.

YADDA AKE CIYARWA

  • Duk azumi daya marar ƙarfi mutum Ɗaya.
  • Ana son dadai abinda zaka iya ciyar da kanka koshi, ba tare da Tsanantawa ba, ba kuma ƙaranci.
  • Ana son kaciyar da irin abinda kuke ci, An tambayi Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya bada amsa, da "kada ku ciyar da su ( marassa ƙarfi ) da abinda ku baku ci" kamar Yanda imam Ahmad ya futar da hadisin, haithami ya ingantashi, Ibn kathi ya kafa hujja da shi cikin Tafsrin sa, ƙarƙashin [267 baƙra ].
  • Ana son abada shi a dafe, idan babu dafaffe, abashi da kayan dafawa.

RAMUWAR AZUMI

  • Mustahabbi ne gaggauta ramakon azumi ga dukk wanda ya sha azumi.
  • Idan kwanakin Ramadana mai zuwa su ka rage dai-dai adadin kwanakin daya sha. Wajibi ne ya rama azumi a cikin kwanakin kafin Ramadan ya kama. 
  • Ba'a so mutum ya yi jinkirin rama azumi har wani Ramadana ya zagayo, ba tare da wani karbabben uzuri kamar rashin lafiya. Idan yayi haka ya saba umurnin Allah. Don haka zai rama adadin kwanakin da ya sha, kuma zai ciyar da miskini a duk kwanakin.

Wannan shine abin da Imam Malik, Imam Shafi da Imam Ahmad, da sauran mayan malaman sun tafi akai, tare da hujja da Hadisin Ibn Abbas wanda Darul Kudiniyyu ya ruwaito: “Wanda ya yi sakacin ramakon azumin Ramadana, har wani Ramadana ya za gayo bai rama abinda ya sha ba, to, ya rama kwanakin da ya sha kuma ya ciyar da miskini a ko wane yini”.

Comments