Azumi da Ramuwa ga Mara lafiya da matafiyi

Allah yana cewa "Kuma wanda ya kasance marar lafiya ko cikin tafiya sai yayi adadin wasu kwanakin (daidai yawan wadanda ya sha)" Bakara aya ta 185

  • Idan mara lafiya, ko matafiyi yazama bazai wahala ba idan yayi Azumi, to yin azumi shi yafi.
  • Amma idan matafiyi, ko mara lafiya yazama cewa idan sukayi azumi zasu wahala to barin Azumin shine yafi. Yazo a hadisi daga سعيد الحذري رضي الله عنه. Yace: Hakika mun kasance muna tafiya zuwa yaki alokacin watan Ramadan tare da manzon Allah saw. acikin akwai masu yin azumi, akwai kuma wadanda basa yin azumi maana suna cin abinci, domin kada su sami mushaqqa.
  • Mustahabbi ne gaggauta ramakon azumi ga dukk wanda ya sha azumi.
  • Idan kwanakin Ramadana mai zuwa su ka rage dai-dai adadin kwanakin daya sha. Wajibi ne ya rama azumi a cikin kwanakin kafin Ramadan ya kama. 
  • Ba'a so mutum ya yi jinkirin rama azumi har wani Ramadana ya zagayo, ba tare da wani karbabben uzuri kamar rashin lafiya. Idan yayi haka ya saba umurnin Allah. Don haka zai rama adadin kwanakin da ya sha, kuma zai ciyar da miskini a duk kwanakin.
Wannan shine abin da Imam Malik, Imam Shafi da Imam Ahmad, da sauran mayan malaman sun tafi akai, tare da hujja da Hadisin Ibn Abbas wanda Darul Kudiniyyu ya ruwaito: “Wanda ya yi sakacin ramakon azumin Ramadana, har wani Ramadana ya za gayo bai rama abinda ya sha ba, to, ya rama kwanakin da ya sha kuma ya ciyar da miskini a ko wane yini”.

Comments