Azumin Bakance

Ma'anar Azmin Bakance

Shine Azumin Daukan Alkawari ga Allah idan ya baka wani abu, ko wani burin ka ya cika zakayi azumi.

Adadin Azumin bakance; mutum shi yake kayyade adadin Azumin da zai yi lokacin daukar Alkawari, misali zan yi azumi 7 idan Allah ya bani kaza.

Bada iya azumin ake bakance ba; wani zai iya cewa zai yi sallar nafila kaza ko zai yi yanka domin Allah.

Hukuncin sa wajibi ne; yana wajaba ga duk Wanda ya dau alkawari yin azumi idan Allah ya cika masa wani burinsa, ya cika alkawarin sa, ma'ana yayi azumin.

حَدَّثَنَا أَبُو نُعَيْمٍ، حَدَّثَنَا مَالِكٌ، عَنْ طَلْحَةَ بْنِ عَبْدِ الْمَلِكِ، عَنِ الْقَاسِمِ، عَنْ عَائِشَةَ ـ رضى الله عنها ـ عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ ‏ "‏ مَنْ نَذَرَ أَنْ يُطِيعَ اللَّهَ فَلْيُطِعْهُ، وَمَنْ نَذَرَ أَنْ يَعْصِيَهُ فَلاَ يَعْصِهِ ‏"‏‏.‏

Daga Nana Aisha Allah ya yarda da ita tace mazon Allah saw yace " Wanda yayi Bakancen yin wani Abu na bin Allah to Lallai yayi shi, Wanda kuma yayi Bakancen yin wani Abu na sabon Allah to kar yayi shi" Sahihul Bukhari 6696.

Yadda ake yin sa; shidin kamar sauran Azumi yake, abinda yake haramta ga duk mai Azumin farilla ko nafila yana haramta ga mai Azumin bakance, kamar ci ko sha ko jima'i, da duk ayyukan da zasu kusantaka da su, ko da sabon Allah.

Wallahu A'alam!

Comments