Azumin Kaffarar rantsuwa

Kaffarar rantsuwa, tana nufin maye gurbin rantsuwar da aka dau alwashi a zuciya kuma aka kasa cikawa.

Wato ana kaffarar rantsuwa ne a rantsuwar da aka dau alwashi a zuciya, sannan aka kasa cika shi.

Abin lura 

Akwai ire-iren rantsuwa wanda ba na alwashi ba, to wayannan rantsuwar ba'a yi musu kaffara. Amma suma suna da nasu hukuncin. 
Wayannan rantsuwar sune;

  • Yasasshiyar Rantsuwa; ita ce rantsuwa da mutum zaiyi ba tare da tabbatar da ita a zuciyarsa ba. Misali Eh wallahi, ko A’a Wallahi.
Hukunci ta; Ba'a son irin wannan rantse rantsen. Amma ba kaffara a kansu.
  • Rantsuwar Neman yarda; shine mutum ya rantse domin yardar da wani ko wasu. Misali "wallahi bani bane"
Hukuncin ta; yana zama halak idan da gaske yake. Amma haram ne kuma fasikanci, kuma zunubi ne idan karya yake.

Amma rantsuwar alwashi dole ne cika ta, rashin cika ta da wani lalura ko ba lalura to kaffara tana zama dole.

Sai dai wasu maluman suna ga cewa idan Mutum ya katange rantsuwar da Insha’Allah to babu kaffara akansa. Misali Mutum yace: Wallahi bazan yi kaza ba Insha’Allah. Ko wallahi zanyi kaza Insha’Allah.

Yadda ake kaffarar rantsuwa

Allah yana cewa "Allah ba ya kama Ku da yassasun rantse-ratsenku sai dai yana kama ku da abin da kuka kulla rantsuwa a kansa, sannan kaffararsa ita ce ciyar da muskinai goma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyalinku (dashi), ko tufatar da su, ko kuma 'yanta wuyaye, sannan Wanda bai sami (yin wadancan ba) sai (yayi) Azumin kwana uku. Wannan shi ne kaffarar rantsuwarku idan kun rantse. Ku kuma kiyaye rantse-rantsenku. Kamar haka ne Allah yake bayyana maku ayoyinsa din ku  gode". Ma'ida ayaa 89

Acikin wannan ayar Allah ya bada zabin kaffara ga mai rantsuwar alwashi kamar haka;

  1. Ciyar da Miskinai goma: Za’a dafa abinci a baiwa ko wani miskini daidai da abinda kake ciyar da kanka.
  2. Tufatar da Miskinai goma: za’a tufatar da miskinai goma. Kowa za’a bashi tufar da zata ishe shi yin Sallah aciki.
  3. Ƴanta Bawa ko baiwa Mumina: Na uku shine ƴanta bawa ko baiwa mumini.
  4. Yin Azumin kwana uku a jere: wannan shine idan Mutum bai samu daman yin wayancen abubuwa ba sai yayi Azumi uku.


Comments