Ma'anar Azumi Hukincin sa Da yadda Ake yin sa

 Mene Azumi

A yaren larabci; yana nufin Kamewa da barin wani abu.

A Shari’a; Shi ne bautawa Allah ta hanyar kamewa daga cin abinci da Abin sha da jima’i, tun daga hudowar alfijir har zuwa faduwar rana.

Matsayin Azumin; 

Azumi yana da matsayin wajibi, Mustahabbi, da makrohi.

WAJIBI; Azumin daya zama dole, ana samun lada ga yin sa, ana samun zunubi ga barinsa. Gasu kamar haka;

  • Azumin Ramadan wajibi ne; kuma yana daga abubuwa biyar da aka gina musulunci dasu.
  • Azumin bakance; shima wajibi ne, ga wanda ya dau Alqawari ga Allah, misali zai yi Azumi kaza idan ya samu kaza.
  • Azumin kaffara; shima wajibi ne, ana yi don Maye gurbin Azumin da aka bari kamar Ramadan, ko barin wani aiki, misali wanda bai samu abun yanka ba bayan tamattu'i. ko aikin sabo misali kisan kai bisa kuskure, da karya rantsuwa.

MUSTAHABBI; shi ne dukkan azumin da shari’a take so a yi wanda akwai lada a yinsa amma ba zunubi ga barin shi, kamar azumin ranar Litinin da Alhamis, da azumin kwana uku a kowane wata, da azumin ranar Ashura, da azumin goman farko a cikin watan Zulhijjah, da azumin ranar Arafa. 

MAKROHI; Azumin da ba'a son yi sa, shine kamar Azumin ranar idi, da ranar Arfa gamai hajji, da ranar juma'a ba tare da hada ta da ranar alhamis ko asabar ba


Wa'yanda Azumi yake wajaba akan su

Azumi yana wajaba a kan dukkan musulmi, baligi, me hankali, da lafiya namiji ko mace.

Hukuncin Wanda baya Azumin Ramadan

Wanda baya Azumin Ramadan ya kafurta, dumin Azumi yana daga rukunnan musulunci guda biyar wanda mutum baya cika cikakkyen musulmi sai da su.

Yadda ake Azumi

  • Niyyar Azumi; ya wajaba a kwana da niyyar azumi tun da daddare idan azumin na wajibi ne, amma idan azumin nafila ne to ba wajibi ba ne, saboda ya inganta a yi niyyar azumin nafila da rana indai bai y abin da yake karya azumi ba, (kamar ci ko sha). Saboda abin da aka rawaito daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, “Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya shigo wata rana, sai ya ce, “Ko kuna da wani abin ci? Sai Muka ce, “A’a” sai ya ce, “To ina azumi”(1). 
  • Barin Ci da Sha da jima'i; duk da wannan abubuwan suna zama halak a rayuwar yau da kullum, amma haram ne ga duk wanda yake azumi, haka zalika haram ne aikata duk abin da zai iya kai shi gare su. Tun daga bellowar Alfijir har zuwa faduwar rana.
  • Nesantar Zunubai; me Azumi ya zama dole ya gujewa aikata zunubai da dukkan gabban sa, daka kanana har manyan zunubai. Zai kiyaye bakin sa daga Gulma, Munafurci, kalaman batsa, da sauran abin da Allah ya haramta aikatawa da baki. Ido kuma daga kallon tsiraici a fili ko a hutuna ko video. Hannaye; daga duk wani zunubi kamar caca, sata, zalunci da sauran su. Kafafuwa, daga tafiya zuwa ga zunubi.
  • Kusantar ayyukan lada; kamar yadda me Azumi zai gujewa zunubai haka zai kusanci ayyukan lada da dukkan gabban sa da lokacin sa gurin yawan sallah, karatun Al'qurani, anbaton Allah (tasbihi), salatin Annabi (saw) kyutatawa Iyaye, da iyali, sadar da zumunci, da Neman halak, Sadaka, da temako.


Comments