Ma'anar zihari da kaffarar sa


Ma'anar Zihari da inda ya samo Asali

 shine kamanta matarka da mahaifiyar ka, ta fuskar haramci.

Misali “Kin haramta gare ni yadda gadon bayan mahaifiyata ta haramta gare ni

Wannan wata al'ada ta ta jahiliyya, wacce take da matukar muni. A lokacin jahiliyya maza sunawa matansu haka idan suna son rabuwa da su.

Hakika wannan mummunar magana ce da kuma karya. Allah yana cewa "wadanda suke yin zihari daga cikinku ga matansu (watau su kwatanta matansu da iyayensu), su ba iyayensu mata bane; iyayensu mata su ne wadanda kawai suka haife su. Hakika kuma au lallai suna fadar muguwar magana ne da tsagworan karya, kuma hakika Allah lallai mai rangwami ne mai gafara."

An samu wane sahabin mazon Allah saw Wanda ake kira Ausu bin Samith yayiwa matarsa Haulatu bint Sa'alabata zihari.

Wanda yana nufin rabuwarsu har abada, hakan yasa takai kara ga mazon Allah (saw) tana nanata bakin cikin ta, sai Ayoyi suka sauka dauke da hukunci da kuma nuna haramci da munin irin wannan firuci ga masulmi.

Allah yana cewa "Hakika Allah ya ji zancen wadda take tantaunawa da kai game da (lamarin) mijinta, tana kuma kai kara zuwa ga Allah, Allah kuma yana jin tantaunawarku. Hakika Allah mai ji ne mai gani".

Kaffarar zihari

Me zihari zaiyi kaffarar domin ci gaba da zama da matarsa.

Kamar yadda Allah ya bada zabi a Al'qurani yake cewa; "Wanda kuwa suke yin zihari ga matansu sannan suka yi niyyar janye abin da suka fada, to sai su 'yanta wuyaye (watau bawa namiji ko mace), run kafin su sadu wannan ana yi muku wa'azi game da shi, kuma masanin abin da kuke aikatawa ne".

Sannan wanda bai samu ba, to sai ya yi azumin wata biyu a Jere run kafin su sadu. Sannan wanda bai samu iko ba, sai ya ciyar da miskini sittin. Wannan kuwa din Ku ba da gaskiya da Allah da manzonsa. Wadannan kuma su ne iyakokin Allah. Kafirai kuma suna da azaba mai radadi".

Acikin wannan ayar Allah ya bada zabin kaffara ga Wanda yayi Zihari kamar haka;

  1. Ƴanta Bawa ko baiwa Mumina: Na farko shine ƴanta bawa ko baiwa mumini yana haramta ya kusanci matar sai bayan ya yanata baiwar ko bawan.
  2. Yin Azumin kwana sittin a jere: wannan shine idan Mutum bai samu daman yanta bawa ko baiwa ba sai yayi Azumi sittin, kuma yana haramta ya kusanci matar sai bayan ya gama Azumin.
  3. Ciyar da muskinai sittin; mataki na uku shine ciyar da miskinai sittin ga wanda baya iya azumi, yana haramta ya kusanci matar sai bayan ya gama ciyarwar.

Abin lura

Haramun ne ya kusanci matar sai bayan ya gama kaffara. 


Comments