Sallolin Farillah

 Menene Sallar Nafila

Ma'ana

Sallar Nafila; a yare na nufin; Dadi/Kari

A gurin malamai kuma na nufin; sune sallolin daba na farilla ba, sallah nafila ita ce sallar kari, wacce Allah ba farlanta ba akan ko wanne musulmi.

Ita ce Sallar daba ta farilla ba ba kuma wajibi ba.


Sallar nafila ta kasu kaso biyu;

  • Alrawaatib (Nafilolin da suke bin farillai); sune sallolin da akeyi kafin ko bayan sallolin farilla. Lazimtar wayannan salloli sunna ce mai karfi. Yazo a hadisi Daga Uwar Muminai Ummu Habiba R.A tana cewa: "Naji Manzon Allah s.a.w yana cewa”;- " Babu wani bawa musulmi da zai yi salloli raka’a goma sha biyu ga Allah a kowane rana,na nafila ba farilla ba,face sai Allah ya gina masa gida a aljanna"صحيح مسلم : رقم (728).' Akwai;


  1. Raka'a Hudu kafin Azzahar, Daga Khãlid daga Abdillahi bn Shaqiq yace: Na tambayi Nana A’isha R.A game da Sallar Annabi s.a.w ta nafila sai tace:- Manzon Allah s.a.w ya kasance yana yin sallar nafila raka’a hudu a gidansa kafin sallar azzahar,sannan sai yafita zuwa masallaci yayiwa mutane sallah,sannan ya shigo gida yayi raka’a biyu bayan Sallar azzahar. ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ
  2. Raka'a biyu bayan Azzahar, Manzon Allah s.a.w ya kasance yana yin sallar magariba da mutane,sannan sai shiga gida yayi nafila raka’a guda biyu. ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ
  3. Raka'a biyu bayan magriba, Manzon Allah s.a.w ya kasance yana yin sallar magariba da mutane, sannan sai shiga gida yayi nafila raka’a guda biyu. ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ
  4. Raka’a guda biyu bayan Isha’i Manzon Allah s.a.w ya kasance, idan yayiwa mutane sallar Isha’i yana shiga gidan sai yayi sallar nafila raka’a guda biyu. ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ
  5. Rak’a guda biyu kafin sallar Assuba; Nana A’isha R.A taci gaba da cewa: "Manzon Allah s.a.w ya kasance idan alfijir ya fito,yana yin raka’a biyu” صحيح مسلم-رقم:(730).

  • Gairu-Rawaatib (Wanda basa bin sallolin farilla); wannan suna da yawa, akwai Sallar 

  1. Sallar duha; ana yinta bayan ɓullowar rana, da safe, a ƙalla raka'a biyu.
  2. Sallar wutiri; ana yinta bayan sallar isha'i mafi ƙarancinta raka'a ɗaya, yawan ta rak'a goma sha ɗaya 11, ayi biyu ayi sallma har ya rage ɗaya a ƙarshe ayita, ayi sallama. Koda anyi fiye da sha ɗayan (11) babu laifi amma dai a ƙarshe ayi witiri wato a rufe da raka'a ɗaya, ayi sallama.
  3. Sallar tarawihi; (Asham) sallar nafila ce da ake yinta bayan sallar isha'i a cikin watan Ramadana ana yinta raka'a 11
  4. Sallar idi; Karin bayani akan Sallar Idi
  5. Sallar Neman ruwa (salatul istiska'a
  6. Sallar gushewar hasken rana ko wata (salatul khusufi). Karin bayani akan sallar chanzawa hasken rana ko wata (salatul khusufi)


Muna maraba da shawarwarin Ku, da kuma gyararrakin Ku, domin anfanar musulmi baki daya🙏

Comments