Sallah da Hukunce-Hukuncen ta A Musulunci

Mene sallah? 

Sallah a yare na nufin "Addu'a" 

Amma a addini tana nufin bautarwa Allah ta hanyar ayyuka da kalamai kebantattu, wacce ta hade tsatuwa ruku'u da sujjada da zama, da anbaton Allah, ana fara ta da kabbara a rufe da sallama.

Matsayin sallah A musulunci

Sallah wajibi ce; kuma tana daga abubuwa biyar da aka gina musulunci dasu.

Wa'yanda sallah ta wajaba akan su

Sallah ta wajaba a kan dukkan musulmi, baligi, me hankali namiji ko mace.

Hukuncin Wanda baya sallah

Wanda baya sallah ya kafurta, dumin sallah tana daga rukunnan musulunci guda biyar wanda mutum baya cika cikakkyen musulmi sai da su.

Yadda Annabi (saw) yake sallah

Annabi (s.a.w) yana cewa: "Kuyi sallah kamar yadda ku kaga inayi" (Muslim: 631).

Sabi da haka ya zamo dole musulmi yayi sallah yadda annabi saw yayi. 

  • Fuskantar Alkibla; abin da ake son mutum ya fara a sallah shine fuskantar Alkibla (ka'abah)
  • Sanya sutura (shamaki) da kusantar ta; sannan ya Santa sutura, Ana son ya kasance tsakanin ka da suturar kamar a Zira'I uku, sutura kuma ta zama kamar tsowon zira'i, tsakanin yadda zaka sanya goshin ka da kuma da sutura ya zamo gwargwadon yadda akuya zata iya wucewa. 
  • Yin niyya a zuciya; kudurce zakayi Sallah kaza domin neman yardar Allah a zuciya, ya wadatar ga mai Sallah. 
  • Yin kabbara; "Allahu akbar ". Zaka daga hannayen ka kafin kayi wannan kabbarar, ko tare da kabbarar, ko bayan kayi kabbarar, zuwa saitin kafadun ka ko kunnuwan ka, tare da mike yatsun ka da fuskantar da su zuwa alkibla
  • Daura hannayen ka a kirjin ka; Ana son hannun dama ya kasance akan na hagu, ko ka damke hannun hagu.

  • Kallon wajen sujjadar ka; sannan anason mutum ya kalli wajan sujjadar, ba tare da sunkuyar da kai ba, ba kuma a so mutum ya daga kansa yayi sama.
  • Yin addu'ar bude sallah; kace"Subhanakal laahumma wa bihamdika, wa tabarakas muka, wa ta'aalaa jadduka, wa laa ilaaha gairuka". Ko kace: "Allahumma baa'id bainii wa baina khadhaayaya kama ba'adta bainal mashriqi wal magribi, Allahumma naqqinii min khadhaayaya kama yunaqqath thaubul abyadhu minad danas, Allahuummag silnii min khadhayaya bith thalji wal barad". Sai kace: " A'uuzu billaahi minash shaidanir rajiim ".
  • Karatun Fatiha; Sai ka karanta surar fatiha, tare da tsayuwa a kashen kowace aya, in ka gama kace "Ameen" Abin nufi Allah ka amsa. Wadda kuma amin din sa ta dace da ta mala'iku, to an gafar ta masa abinda ya gabata na zunuban sa kamar yadda annabi (s.a.w) ya fada. Zaka karanta surar fatiha a cikin kowace raka'a ko da kai mamu ne, a lokacin da liman ya ke asirta ta, ko kuma lokacin da baka jin karatunsa. Zaka karanta Fatiha ita kadai a rako'oin biyu na karshen; Azzahar, la'asar, isha'I, da kuma raka'a ta uku ta sallar magariba.
  • Karatun Sura; Yana daga sunnah ka karanta sura ko kuma yana daga sunnah karanta wani sashin alkur'ani a raka'o'i biyun farko bayan Fatiha. Bayan ka gama karatu, zaka dan yi shiru kafin kayi ruku'u, gwargwadon yadda nunfashin ka zai koma.

YADDA AKE RUKU'U

Bayan haka sai ka tafi zuwa ruku'u, tare da yin kabbara da kuma daga hannayen ka zuwa saitin kafadar ka ko kuma kunnuwan ka.

  • Sanya hannayen ka akan gwiwoyin ka, da damke gwiwoyin da su.
  • Bude tsakanin yatsun ka na hannu. Ba'a so mutum ya tsuke yatsun hannun sa.
  • Nesantar da hannayen ka; daga jikin ka. 
  • Mikar da bayan ka, yadda idan da za'a zuba ruwa zai zauna, ka sanya kanka dai-dai da bayan ka.
  • Fadin"Subhana rabbiyal aziim" ( sau uku ). Ko: "Subhaakal laahumma rabbana wa bihamdika, allahummag firlii". Sannan babu laifi bayan haka ka kara ya domin yin sujjada.

YADDA AKE SUJJADA

  • Fara sanya hannayen ka a kasa; abin da zama fara yi a sujjada shine kai hannayen ka zuwa kasa. 
  • Yin sujjadar akan tafukan hannaye; da gwiwoyin kafa, da kan yan yatsun kafa, da kuma hanci da goshi.
  • Sanya tafukan hannayen ka a saitin kafadun ka; ko kuma kunnuwan ka. 
  • Daga zira'in hannayen ka daga kasa; ba'a son zara'in hannayen ka su kwanta a kasa, ana son ka daga su sannan ka buda su.
  • Hada diga-digan ka; da kuma tabbatar da kan yatsun kafar ka a kasa, da fuskantar da su zuwa alkibla.
  • Nesantar da damatse; ka ne santar dasu daga jikin ka.
  • Nutsuwa; ana son mutum ya nutsu, ya tattaro hankalin sa guri daya.
  • Tasbihi; Fadin: "Subhaana rabbiyal aalaa"(sau uku). Ko: "Subhanakal laahumma rabbana wa bihamdika, Allahummag firli".
  • Dagowa daga sujjadar farko; tare da fadin "Allahu Akbar".

Zaman tsakanin sujjidu biyu

Sannan ka zauna har sai kowane sashi ya koma makomar sa. Sannan irin zaman da za kayi shi ne: 
  • Ka shinfida kafar ka ta hagu; kazauna a kan ta, kafar dama kuma ka kafata, yatsunta kuma su fuskanci alkibla. Ko kuma ka kafa kafafun ka, kazauna akan diga digan su. 
  • Sai kuma ka daura hannun ka na dama akan cinyar ka ko gwiwar ka; haka na hagu ma, tare da shinfida yatsun su.  
  • Yin Tasbihi a zaman; Sannan yace "subhana rabbiyal aziim " (sau uku). Ko: "Subhanakal laahumma rabbana wa bihamdika, allahummag firlii ".  Ko kace: "Rabbigfir lii, war hamnii, wahadini war zuqnii, war fa'anii".
  • Komawa sujjada ta biyu;  kuma kayi sujjada ta biyu kana mai fadin: "Allahu Akbar", kayi ta kamar sujjadar ka ta farko da kayi.
  • Sannan ka dago zuwa raka'a ta biyu; ana so ka dan zauna kafin ka mike, sannan ka mike akan hannayen ka a dunkule zuwa raka'a ta biyu. Zaka yi duk abinda kayi a raka'ar farko a cikin wannan raka'ar, banda kabbarar harama da addu'ar bude sallah. Sannan ana so kar ta kai ta farko tsayi.
  • Zaman tahiya; Bayan kagama wannan raka'ar sai kuma kayi zaman tahiya.

YADDA AKE ZAMAN TAHIYA

  • ka daura hannayen ka kamar yadda kayi a tsakanin sujjada biyu; yatsun ka na hannun dama zaka dunkule su, ko ka daura babbar yatsar ka akan ta tsakiya, banda manuniya ita zaka yi nuni da ita zuwa alkibla
  • Kada dan yatsa; Sai kuma kana kada yatsar taka manuniyar, ko a kuma ka tsaida ita, ka kuma sanya kallon ka akan ta
  • Karatun tahiya; zaka karanta tahiya kace; "Attahiyyaatu lillaahi, wassalawaatu, wadhayyibaatu, assalamu alaika, ayyuhan nabiyyu, wa rahmatullaahi wa barakaatuhu, assalaamu alainaa wa alaa ibadullahis saalihiina, ash-hadu allaa ilaaha illallaahu, wa ashhadu anna muhammadan abdu sanan 
  • Salati ga annabi  kace; "Allahumma salli alaa Muhammad, wa alaa ali Muhammad kamaa sallaita alaa Ibrahim, wa alaa aali Ibrahim, innaka hamidum majid, Allhumma barik alaa muhammad, wa alaa aali Muhammad, kamaa barakta alaa Ibrahim, wa alaa aali Ibrahim innaka hamidum majid".
Abin lura; Idan sallar wacce ake raka'a biyu ce sai kayi adu'o'in da za su zo sannan kayi sallama. Idan kuma wacce ake raka'a uku ce ko hudu, sai ka mike bayan ka gama yiwa annabi (s.a.w) salati, kamar yadda ka yi a lokacin mikewar ka zuwa raka'a ta biyu. Sannan ka karanta surar fatiha, kayi ruku'u da sujjada kamar yadda su ka gabata, sannan ka zauna domin yin tahiyar karshe idan a sallar magriba ce, idan kuma sallar wacce ake raka'a hudu ce, sai ka mike bayan kayi irin abinda kayi a lokacin mikewa zuwa raka'a ta biyu.
Bayan ka gama raka'o'i sai kuma ka zauna domin yin tahiyar karshe. 

ZAMAN TAWARRUKI A TAHIYYAR KARSHE

Ana so kayi zaman tawarruki a zaman ka na tahiyar karshe, yadda ake yin sa shi ne:

  • Sannya mazaunin ka na hagu a kasa; sannan ka fitar da kafar tagefen dama, kafar dama kuma ka kafata ko ka shinfida ta.
  • Sannan sai kayi addu'o'i kamar haka; Karanta tahiya (kamar yadda ta gabata). Yiwa annabi  (saw) salati (kamar yadda ya gabata). Neman tsari daga abubuwa guda hudu kace: "Allahumma innii a'uuzu bika min azabi Jahannam, wa min azabil qabri, wa min fitnatil mahyaa wal mamaat, wa min sharri fitnatil masiihid dajjal".  Sai kuma kayi addu'o'in da annabi (s.a.w) ya koyar, daga cikin su akwai: "Allahumma innii zalamtu nafsii zulman kathiran, wala yagfiruz zunuuba illaa anta, fagfirlii magfiratan min indika war hamnii innaka antal gafurur rahiim Allahummag firlii maa qaddamtu, wamaa akkhartu, wamaa asrartu, wamaa aalantu, wamaa asraftu, wamaa anta aalamu bihii minnii, antal muqaddimu wa antal mu'akhkhiru, laa ilaaha illaa anta ". Allahumma hasibnii hisaaban yasiira "Ko wasu daga cikin addu'o'in da su ka tabbata a sunnah.
  • Sai kuma kayi sallama; ta gefen ka na dama har sai anga hasken kumatun ka, haka ta gefen ka na hagu ma

YADDA AKE SALLAMA:

Anan kwai nau'ikan sallama guda hudu;
  1. "Assalamu alaikum warahmatullah" ta gefen dama da hagu.
  2. "Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuh", ta gefen dama"Assalamu alaikum warahmatullah", ta gefen hagu.
  3. "Assalamu alaikum", ta gefen dama, "Assalamu alaikum", ta gefen hagu.
  4. "Assalamu Alaikum" sau daya a gaban ka, tare da karkatar da fuskar ka zuwa damacin ka kadan.

Bincika nan domin samun darasi akan wannan.👇

Comments